Amurka da Nuclear Iran | Labarai | DW | 06.04.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka da Nuclear Iran

Jakadan Amurka a komitin sulhun Mdd ya bayyana cewa ,komitin zata bawa Iran dama biyu ne kachal na dakatar da shirin nuclearnta,kafin ta kakaba mata takunkumi.Jakadan Amurka John Bolton yayi wannan furucin,a yayinda yake tabbatar dacewa cimma nasaran amincewa baki daya kann matakan hukunta iran,batu ne mawuyaci.Amurka dai na kokarin ganin cewa ta shawo kann kassashe biyu masu zaunanniyar kujera watau China da Rasha,a dangane da daukan matakan ladabtar da Iran,domin tana fatan samun cikakken baya kann cewa Tehran na kera makaman nuclear.Bolton,wanda keda tsattsauran raayi kann Iran ,yace idan har Iran bata dakatar da sarrafa sinadran uranium zuwa karshen wannan wata kamar yadda mdd ta umurceta ba,babu shakka komitin sulhun na iya kakaba mata wasu matakai masu tsanani,da zasu karkatata.Iran,wadda ya zuwa yanzu jamianta basu mayarwa jakadan Amurkan martanin kalamansa ba,ta sha nanata cewa shirin nucleanta na samar da makamashi ne amma ba makamai ba.

 • Kwanan wata 06.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6z
 • Kwanan wata 06.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6z