1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka da Koriya ta kudu sun sake jan kunnen Koriya ta arewa

October 19, 2006
https://p.dw.com/p/BufI

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice da takwaranta na Koriya ta kudu Ban Ki moon sun gargadi Koriya ta arewa cewa zata fuskanci mummunan sakamako muddin dai ta sake yin wani gwaji na makamin nukiliya.

Wajen taron manema labarai a birnin Seoul Rice tace wannan ziyara da take yi a yankin Asiya,kara tabbatar da sadaukar da kann Amurka wajen kare Koriya ta kudu.

Tace gwamnatin Amurka bata da bukatar yin wani abinda zai kara munana halin zaman zulumi a yankin,musamman saboda bukatar Amurkan na binciken jiragen ruwa masu daukar kaya shiga da fita cikin Koriya ta arewa.

Kudirin takunkumi na da komitin sulhu ya amince a ranar 9 ga watan oktoba,ya amince da gudanar da irin wannan bincike.