Amurka da India sun cimma yarjejeniyar makamashin Nukiliya | Siyasa | DW | 02.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amurka da India sun cimma yarjejeniyar makamashin Nukiliya

Ziyarar shugaban Amurka George W Bush a kasar India ta karfafa huldar danganta a tsakansin kasashen biyu.

Shugaban Amurka George W Bush da P/M India Manmohan Singh

Shugaban Amurka George W Bush da P/M India Manmohan Singh

Shugaban Amurka George W Bush tare da P/M India Manmohan Singh sun cimma wata muhimmiyar yarjejeniya da suka baiyana da cewa gagarumar nasara ce, wadda kuma ta kawo karshen tsawon lokacin da kasashen biyu suka shafe suna tattaunawa a game da dangantaka ta cudanni in cude ka, ta fuskar makamashin nukiliya. Yarjejeniyar da shugabannin biyu suka kulla, za ta bada damar dage tarnakin da Amurka ta yi wa India wanda ya shafe tsawon shekaru 30, bayan da Indian ta yi gwajin makamin ta na nukiliya a shekarar 1974. Bugu da kari yarjejeniyar za kuma ta share faggen yin musayar fasahar nukiliya na lumana da kasar ta India.

A taron yan jarida da shugabannin suka gudanar, sun baiyana yarjejeniyar da cewa za ta bada damar ciyar da kasashen biyu gaba domin cin moriyar makamashin na nukiliya na lumana don amfanin alúmomin su tare kuma da karfafa huldar dangantaka tsakanin Amurka da India.

Sun kuma amince da kaddamar da wani shirin hadin gwiwa don bunkasa harkokin kasuwanci dana tsaro da lafiya da kuma ayyukan gona. Bush yace kulla yarjejeniyar ya zama wajibi domin abu ne da zai amfani alúmomin su. A jawabin sa P/M India Manmohan Singh, yace ya yi matukar farin ciki da cimma daidaito da suka yi na aiwatar da yarjejeniyar cudanni in cude ka da kasashen biyu suka kulla a ranar 18 ga watan July na shekara ta 2005, yana mai cewa a yanzu ya rage ga gwamnatin Amurka ta yi gyara ga dokar kasar ta a game da tanade tanaden dake karkashin yarjejeniyar

A nasa bangaren shugaban Amurka George W Bush ya ce a yau sun cimma muhimmiyar yarjejeniya mai matukar amfani, wanda ya zai taimaka wajen magance matsalolin muhalli, yace a yanzu zaá sami karancin dangwalon masanaántu dake gurbata muhalli,inda ya kara da cewa ya yi Imani gwamnatin kasar India da gaske take. Bisa cimma wannan Yarjejeniya dai, ya zama wajibi ga Bush ya nemi amincewar majalisar dokokin Amurka tare da neman goyon bayan kasashe 45 dake samar da makamashin nukiliyar su yi muámala tare da musayar fasaha da kasar India.