1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurikawa sun shirya zanga-zangar adawa da yaƙin Irak

September 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuBK

Dubun -dubunan jama´a a ƙasar Amurika, sun shirya zanga-zanga ,gaban fadar White House, domin nuna adawa da yaƙin da shugaba Geoerge Bush ya ƙaddamar a ƙasar Irak.

Wannan zanga zanga, ta wakana kwanaki 3 bayan da shugaban ya bayyana aniyar sa ta fara janye dakarun 21.500, daga jimlar sojojin Amurika dubu 168, a shekara mai kamawa.

A cewar wanda su ka shirya wannan zanga-zanga, jamia´an tsaro sun kame mutane kussan 200.

Wannan su ka tada wannan bori, sun yi ta rera kalamomi wanda ke bayyana buƙatar tsige shugaban Amurika daga karagamar mulki.

A cen ƙasar ta Irtak kuwa, a jiya Amurika ta ƙara assara soja ɗaya,wanda shine cikwan sojojin Amurika na 3.773 da su ka rasa rayuka, tun daga mamaye ƙasar Irak a shekara ta 2003 zuwa yanzu.

A fagen siyasar ƙasar kuwa, Praminsita Nuri Al Maliki na ƙara dumuya cikin halin ƙaƙa ni kayi, bayan shawara da yan majalisun dokokin jam´iyar UIA ta Moktada Sadr su yanke ta fita daga rukunin jam´iyu masu bada goyan ga Praministan.

A sakamkon wannan mataki, a halin yanzu Praministan Nuri Al Maliki, ba shi da rinjaye a Majalisar Dokoki.