Amurikawa na matsa kaimi ga Shugaba Bush | Labarai | DW | 27.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurikawa na matsa kaimi ga Shugaba Bush

A kasar Iraki kamar yada aka saba kullum, hare haren kunar bakin wake na ci gaba da hasada mutuwar jama´a a ko wace sahia.

Da assubahin yau, wata mota shake da nakiyoyi ta tarwatse gapp da wucewar wasu ayarin motocin Amurika a birnin Bagadaza.

Mutum daya hwara hulla ,ya rasa ransa, da kuma 8 da su ka sami mumunan raunuka.

A ranar jiya laraba kuma, sojoji 2 ne na Amurika su ka sheka lahira.

A cen kasar ta Amurika shugaba Georges Bush na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga masu adawa da siyasar gwamnatin sa, a game da kasar Iraki.

Amurikawa na kara tofin Allah wadai, ga gwamnatin Bush tun ranar asabar, bayan da yawan sojojin Amurika da su ka rasa rayuka a kasar Iraki, su ka kai dubu 2.

Kafofin sadarwa na kasar sun yayata wannan batu, inda har ma wasun su, su ka jera illahirin sunayen sojojin da su ka mutu da hotunan su, abinda ya kara harzuka amurikawa.

A nasa gefen shugaba Georges Bush na kara ci gaba da bada hakuri ga jama´a, tare da nuna masu wajibcin gudanar da yakin na Iraki.