Amurika ta sa jan biro ga kudaden wasu kampanoni da mutane na Zimbabwe | Labarai | DW | 24.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurika ta sa jan biro ga kudaden wasu kampanoni da mutane na Zimbabwe

Shugaban Bush na Amurika, ya bayana saka takukumi, ga kudaden wasu mutane 128 da kampanoni 33 na kasar Zimbabwe, dake bankunan Amurika, bayan ya zarge su da hannu a cikin taka hakokin jama´a a kasar Zimbabwe ta hanyar mara wa shugaban kasa Robert Mugabe baya ,ya na cinkaren sa babu babbaka.

Cemma, tun watan maris na shekara ta 2003 Amurika ta sa jan biro, ga magudan kudade da Robert Mugabe ya jibge a bankunan Amurika, tare da Karin wasu mutane 77 masu fada a ji a Zimbabwe.

Kakakin gwamnatin Amurika, Dana Perino ya shaida cewa mataki daya da zai daidaita al´amura tsakanin Amurika da Zimbabwe ,shine gwamnati Mugabe, ta mutunta hakin jama´a ta kuma shinfida tsarin mulkin demokradiya inganttace.

Amurika ta jaddada bacin rai a game da murdiyya da gwamantin Zimbabwe tayi a zaben watan Maris na shekara da mu ke ciki, da kuma wargaza gidajen tallakawa a watanin baya, wanda ya jawo tabarbarewar rayuwa a wannan kasa.