1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurika ta cire takunkunmin kuɗin Korea ta Arewa

June 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuIt

A wani mataki na kawo ƙarshen rikicin makaman nuklear Korea ta Arewa,ƙasar Amurika, ta bada sammacin sakin kuɗaden Korea ta Arewa da ta sakawa takunkumi.

Daga jimlar dalla milion 25 da aka sawa takunkumin,Korea ta Arewa, ta karɓi dalla milion 20 a yau alhamis.

Sannan zata karɓi ragowar dalla milion 5, a kwanaki masu zuwa.

A tantanawar da ake yi, a game da batun nuklear Korea ta Arewa, hukumomin Pyong yang, sun gitta sharaɗin sai Amurika ta yi belin wannan kuɗi, kamin su amince da watsi da matakin mallakar makaman nuklea.

Wani kakakin gwamnatin Korea ta Arewa ,ya ce a sakamakon samun wannan kuɗi , babu shakka Korea ta Arewa, zata cikka alƙawurin da ta ɗauka a lokacin tantanawar.