Amurika ta bayyana yiwuwar fara janye sojojin ta daga Irak | Labarai | DW | 06.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurika ta bayyana yiwuwar fara janye sojojin ta daga Irak

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice da takwaran ta mai kulla da harakokin tsaro Robert Gates, sun bayyana rashin gamsuwa a game da gwamnatin ƙasar Irak.

A wata da yan jarida jiya Robert Gates ya yi Allah wadai da matakin da majalisar dokokin ƙasa ta ɗauka na shiga hutun wata guda.

A cewar sa hutu bai dace ba a halin yanzu ga Majalisa, ta la´akari da tashe-tashen hankullan da ke wakana ba dare ba rana.

A wani mataki na ba zata Robert ya bayana yiwuwar fara janye dakarun Amurika daga Irak, kamin ƙarshen wannan shekara.

Daga farkon yaƙin Irak a shekara ta 2003 zuwa yanzu, Amurika ta yi asara sopjoji 3 sannan wasu dubbunai sun ji mummuna raunuka, wasu kuma sun tabuwar hanakali.

Ita ma Sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleesa Rice , ta sanar da gwamnatin Iraki cewar haƙurin Amurika fa, nan da iyaka, kuma a halin yanzu fadar White House ta fara ƙosawa da tafiyar hawainiyar da ake fuskanta, a yunƙurin kawo ƙarshen rikicin wannan ƙasa.