Amurika da Rasha sun cimma yarjejeniyar rage makaman nukiliya | Siyasa | DW | 08.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amurika da Rasha sun cimma yarjejeniyar rage makaman nukiliya

A birnin Prague Obama da Medvedev sun rattaba hannu kan yarjejeniyar rage mallakkar makaman nukiliya.

default

Harba makamin nukiliya

Ƙasashen Amurika da Rasha sun shiga wani saban babe na dangantaka, sakamakon yarjejeniyar rage makaman nukiliya da shugaba Barack Obama da Dmitri Medvedev suka rattabawa hannu yau a birnin Prague na Jamhuriya Chek.

Cemma bara ne,a birnin Prague  na Jamhuriya Chek,shugaba Barack Obama na Amurika ya gabatar da wani jawabi, inda ya bayyana manufofinsa da tsinkayensa, na rayuwa a duniya ba tare da makaman nukiliya ba.

A wani mataki na cimma wannan buri,a ƙarshen watan Maris da ya gabata, shugaba Barack Obama, da takwaransa Dmitri Medvedev na Rasha suka tunɓi juna ta wayar talho, inda suka yi mahaɗa a birnin na Prague ,domin rattaba hannu  akan wannan yarjejeniya mai mahimmanci ta fannin hana yaɗuwar makaman nukliya.

Amurika da Rasha sun mallaki makaman ƙare dangi masu ƙarfi, wanda a cikin ƙiftawa da bissimilah ko wace ƙasa daga cikin su, kan iya shafe yar uwata daga doron duniya.

A shekara 1991 ƙasashen biyu ,sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta rage yawan wannan makamai masu guba,wada aka raɗawa suna START ,saidai kuma ta zo ƙarshe a shekara 2009.

Bayan lokaci mai tsawo na tattanawa , a ƙarshe dai Amurika da Rasha su amince da sabuwar yarjejeniya.

Shugaban Barack Obama yayi tsokaci game da haka:

Zamu haɗa ƙarfin mu wuri guda, domin yaƙi da yaɗuwar makaman nukiliya, ta yadda wannan mataki zai zama misali ga sauran ƙasashen duniya.

Hausawa kance wai gatanar gizo ba ta wuce ƙoƙi,  ƙasashen da Obama ke magana akai, sun haɗa da Jamhuriya musulunci ta Iran wadda a halin yanzu ake kai ruwa rana, game da shirinta na mallakar makaman nukiliya.

Wayne Merry jami´i ne, a cibiyar hulɗa da ƙetare ta Amurika, ya kuma yin ƙarin bayyani game da manufofin da Barack Obama ke da nufin cimma:

Manufar Barack Obama itace yayi amfani da wannan yarjejeniya domin cimma burruruka guda biyu: na ɗaya ƙulla sabuwar ma´amila ta fahintar juna da ƙasar Rasha, sannan na biyu haɗa ƙarfi da sauran ƙasashen duniya, da kuma Komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya domin matsa ƙaimi wajen hana yaɗuwar makamai masu guba, mussamman ta hanyar ɗaukar matakan bai ɗaya  masu ƙarfi ga ƙasar Iran, domin taka mata birki a shirinta na mallakar makaman nukiliya.

Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin  Amurika da Rasha,zata ɗauki wa´adin shekaru goma,sannan  ta tanadi cewar kowace daga ƙasashen biyu, ta rage yawan randunanta na nukiliya zuwa 1550.

Wannan na nuni da cewar, duk da cigaban da aka samu na kyauttata ma´amilala tsakanin Amurika da Rasha ,har yanzu dai ta ciki na ciki.

A ɗaya wajen wannan yarjejeniya ta wakana kwanaki ƙalilan kamin  Amurika ta karɓi wani mahimmin taron ƙasa da ƙasa wanda zai tattana game da hana yaɗuwar makaman nukiliya.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Umaru Aliyu