Amurika da Britania sun bukaci komitin sulhu ya saka takunkumi ga wasu mutane 4 na Sudan | Labarai | DW | 13.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurika da Britania sun bukaci komitin sulhu ya saka takunkumi ga wasu mutane 4 na Sudan

Amurika da Britania, sun gabatar da takaradar haɗin gwiwa, ga komitin Sulhu na Majaliasar Ɗinkin Dunia.

Wannan takarda, na dauke da sunayen mutane 4, yan kasar Sudan, da ake tuhuma da rura wutar rikicin yakin Darfur.

Amurika da Britania, na bukatar komitin Sulhu, ya saka takunkumi ga mutanen 4, da ba su bayyana sunayen su ba, ga kafofin sadarwa.

Jikadan Amurika a Majalisar Ɗinkin Dunia, John Bolton,ya ce, kamar yadda ka´idojin majalisar su ka tanada, ba za iya bayyana sunayen ba, kamin nan da kwanaki 2.

Sannan daga bisani, in babu kasar da ta hau kujera naki, to a nan take dokar saka takunkumin zata fara aiki, a lokacin ne kuma, za a bayyana sunayen mutanen.

A game da rikicin na Darfur, ƙungiyar tsaro ta NATO kokuma OTAN, ta fara zaman taro, da nufin samar da hanyoyin gaggawa, na tallafawa sojojin ƙungiyar taraya Afrika, da ke shiga tsakanin a yankin Darfur.