Amuka ta amince da kakabawa Iran takunkumi | Labarai | DW | 12.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amuka ta amince da kakabawa Iran takunkumi

Amurka ta amince da kudurin da kungiyyar Eu ta gabatar na daukar matakan kakabawa Iran takunkumi.

A cewar rahotanni kasashen yamman sun dauki wannan matakin ne,bisa dalilin cewa Iran din taki watsi da aniyar ta na mallakar makamin Atom.

Bayanai dai sun rawaito sakatariyar harkokin wajen Amurka CR na cewa nan bada dadewa bane, za´a mika wannan kuduri a gaban kwamitin sulhu na Mdd.

Ana dai sa ran da zarar kwamitin sulhun na Mdd ya amince da wannan kuduri, dokar kakabawa kasar ta Iran takunkumi zata fara aiki ba tare da wani bata lokaci ba.

Babban dai burin wannan mataki na takunkumi shine,a shanyo kann kasar ta Iran, yin watsi da wannan aniya tata.