Amr Mussa ya yi wa majalisar al´umar Kurdawa jawabi | Labarai | DW | 23.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amr Mussa ya yi wa majalisar al´umar Kurdawa jawabi

A jawabin da ya yiwa majalisar al´umar Kurdawa, babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Amr Mussa ya yi kira da kafa wata kasar Iraqi mai ´yan´uwantaka da kuma hadin kai tsakanin al´umominta. Lokacin da yake magana a gaban wakilan majalisar dake birnin Erbil na arewacin Iraqi, Amr Mussa ya sake jaddada muhimmancin dake akwai wajen shirya taron sasantawa tsakanin ´yan shi´a da sunni da kuma Kurdawa kamar yadda kungiyarsa ta ba da shawara. A jiya asabar babban malami ´yan shi´a a Iraqi Ayatollah Ali Al-Sistani ya nuna goyi da bayan shirya wannan taro.