Amr Moussa ya yi suka ga daftarin MDD a kan Lebanon | Labarai | DW | 06.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amr Moussa ya yi suka ga daftarin MDD a kan Lebanon

Sakatare janar na ƙngiyar ƙasashen larabawa Amr Moussa ya soki lamirin daftarin Majalisar dinkin duniya a kann rikicin Lebanon yana mai cewa daftarin ya gaza yin kiran a dakatar da fadan cikin gaggawa. yace yaya zasu amince da wannan daftari ? yana mai cewa mun yi tur da Allah wadai da ragargaza kasar Lebanon. Ya kuma baiyana takaici da garkuwa kuwa da Israila ta yi da kakakin majalisar dokokin Palasdinawa, a wannan hali da ake ciki. yace ko kusa bai dace ba kuma ba zasu lamunta da shi ba.