Amnisty International ta soki ziyara Paul kagame a Canada | Labarai | DW | 25.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnisty International ta soki ziyara Paul kagame a Canada

Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama da Hukumar Amnisty International ,sun nuna rashin gamsu wa, da ziyara shugaban ƙasar Rwanda Paul kagame a ƙasar Canada, bisa gayyatar jami´o´i, da wasu ƙungiyoyi na ƙasar.

Albarkacin wannan rangadi na kwanaki 2, Paul Kagame, ya ziyarci jami´ar Western Ontario , kamin ya halarci wani taro lacca, da jami´o´in su ka shirya.

Amnisty Internatinal, ta bayana takaici, ga wannan gayata, ta la´akari da shugaban Rwanda, yayi kaurin sunan a dunia ta fannin aiwatar da kissan gilla, a kan jama´a.

Sanarwar ta ce, ko dan muttunta, kushewun dubunan mutane, da su ka rasa rayuka, a ƙasashen Rwanda, Burundi, da Jamhuriya Demokradiyar Kongo, a sakamakon yaƙin bassasa, da shugaban Kagame, ya hadasa, ya kamata a ce, wannan jami´o´i, sun soke gayyatar.

Yau ne ranar ta ƙarshe, ta wannan ziyara, wasu gungun ƙungiyoyi ,sun bayyana shirya zanga zanga a birnin Montreal, a yau ɗin,domin nuna rashin amincewa, da wannan ziyara.

Wannan shine karo na farko, da wani shugaban kasar Rwanda ya taba kai ziyara a Canada.