Amnesty tace jamian tsaro a Najeriya suna aikata fyade | Labarai | DW | 28.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty tace jamian tsaro a Najeriya suna aikata fyade

Wani rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International yace yan sanda da sojoji a Najeriya suna aikata fyade da wasu laifuka da suka jibinci haka ba tare da kakkautawa ba saboda gwamnati ta gagara daukar matakan sharia akan wadanda suke aikata wannan laifi.

Kungiyar ta Amnesty ta bada misali da sojoji dake yiwa mata fyade a gaban mazajensu da yayansu,da yadda ake fyade ta hanyar anfani da fassasun kwalabe ga wadanda kuma ake tsare da su,hakazalika da azabtar da yara kanana da iyayensu ke daure.

Darektan kungiyar a Najeriya Kolawole Olaniyan,yace a Najeriya yan sanda basu damu da karar fyade da wasu batutuwa da suka shafi hakan ba,wanda mata suke kaiwa yan sandan,haka kuma baa masu aikata laifin da kyar suke fuskantar sharia.

Kakakin rundunar yan sandan Najeriya Haz Iwendi ya amince cewa,batun fyade babbar matsala ce tsakanin rundunonin tsaro a Najeriya,amma yace gwamnati tana iyaka kokarinta don ganin ta kawo karshensa.