Amnesty ta yi suka ga tsarin kurkukun Iraƙi | Labarai | DW | 13.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty ta yi suka ga tsarin kurkukun Iraƙi

Ƙungiyar Amnesty ta yi Allah wadai ga yadda hukumomin Iraƙi ke tafiyar da harkokin gidajen yarin ƙasar

default

Tambarin ƙungiyar Amnesty

Ƙungiyar kare haƙƙin jama'a ta Amnesty International ta yi kakkausar suka ga tsarin tafiyar da gidajen yarin ƙasar Iraƙi a cikin wani rahoton da ta wallafa. Ƙungiyar ta ce kimanin fursunoni 30,000 ne aka jefa su cikin gidajen yari ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ko kuma ba su damar ɗaukar lauya ba. Akan wannan dalilin ne ƙungiyar ta ce fursunonin ke fuskantar ƙarin yiwuwar azabtarwa da kuma rashin ba su kulawar da ta dace. Ƙungiyar ta Amnesty ta ƙara da cewar hukumomin Iraƙi na jefa mutane cikin gidajen yari na sirri, inda wasunsu kuma suka mutu saboda azabtarwar da aka yi musu a cikin gidajen yarin - kamar dai yadda rahoton ƙungiyar ta Amnesty International, wanda ta fitar a wannan Litinin ya bayyanar. Akan haka ne ƙungiyar ta buƙaci hukumomin Iraƙi a birnin Bagadaza, fadar gwamnatin ƙasar da su kyautata yanayin tafiyar da lamuran da suka shafi fursunonin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Halima Balaraba Abbas