Amnesty ta soki yarjejeniyar EU ta Turkiyya
June 3, 2016Kungiyar mai fafutukar kare hakkin al'umma ta yi wannan roko ne acikin wani bayani data gabatar mai shafuka 35, inda ta ce wannan mataki na Eu bai dace ba domin ya sabawa ka'ida.
A yanzu haka dai kasar Turkiyya na zama mai saukin 'yan gudun hijira miliyan 3, da suka hadar da 'yan Siriya 2.75, kuma tana saran samun karin wasu bisa ga yarjejeniyar da Turkiyyan ta cimma da Tarayyar Turai.
Yarjejeniyar dai ta tanadi cewar dukkan 'yan gudun hijira da suka isa tibirin Girka bayan ranar 20 ga watan Maris, za'a tusa keyarsu zuwa Turkiyya.
A madadain hakan, Turai zata karbi dan gudun hijirar Siriya guda daya daga Turkiyyan. Daura da haka, turkiyya zata ci moriyar kudi euro biliyan 6, tafiye tafiye ba tare da takardar izini ba, tare da gaggauta tattaunawar batun shigar da ita cikin Kungiyar Tarayyar Turai.