Amnesty ta roki MDD ta kare alúmar Dafur | Labarai | DW | 28.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty ta roki MDD ta kare alúmar Dafur

ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta duniya Amnesty International ta buƙaci kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya ya ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuwar alúmar yammacin Dafur daga hallaka a hannun sojojin gwamnatin Sudan. Kungiyar ta kuma yi kira ga kwamitin tsaron ya matsawa fadar gwamnatin a birnin Khartoum amincewa da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar ɗinkin duniya a yankin kan iyakar Sudan da Chadi. A yau ne dai kwamitin tsaron zai gudanar da taro a birnin New York domin tattaunawa a game da wani daftarin ƙudiri a kan Dafur. Mataimakiyar shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bil Adaman da duniya Kate Gilmore, ta ce a kullum gwamnatin Sudan na jigilar sojoji ta jiragen sama zuwa yankin al-Fasher dake arewacin Dafur. Ta ce yan gudun hijirar na Dafur na cikin fargaba kan cewa sojojin waɗanda suka tilasta musu yin ƙaura daga gidajen su, sune kuma ake ƙoƙarin turawa domin tsaron lafiyar su. Shugaban ƙasar Sudan Omar al-Bashir wanda ya bujirewa tura sojojin gamaiyar ƙasa da ƙasa, ya shaidawa sakatare janar na Majalisar ɗinkin duniya Kofi Annan cewa Sudan zata tura dakarun soji 10,500 domin tabbatar da tsaro a yankin Dafur. Jamiár Amnesty Kate Gilmore ta ce akwai maƙarƙashiya a game da shirin gwamnatin Sudan wanda bai kamata a amince da ita ba.