1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta damu da yawan kisa a Najeriya

April 13, 2018

Kungiyar Amnesty International ta koka kan karuwar wadanda ake yanke wa hukuncin kisa a Najeriya yayin da kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara ke kokarin daina yanke hukuncin mai tsanani.

https://p.dw.com/p/2vyCf
Amnesty international
Hoto: picture-alliance/dpa/W.Kumm

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International, ta koka kan yadda ake samun karuwar wadanda ake yanke wa hukuncin kisa a Najeriya, yayin da kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara ke kokarin daina yanke hukuncin mai tsanani.

A cewar kungiyar, a bara Najeriya ta yanke wa mutane 621 hukuncin na kisa, yayin da ake da wasu sama da 2000 da ke fuskantar haka a kasar, alkaluman da suka zarta na kowace kasa a nahiyar Afirka. Alkaluman dai sun karu daga mutum 171 a shekara ta 2015 zuwa 527 a shekara ta 2016, yayin da a yanzu ake da sama da 620.

Kasar Gini, ta daina daukar matakin hukuncin kan kowane irin laifi 'yan kasar suka aikata, kamar yadda kasashe irinsu Chadi da Burkina Faso suka dauki matakin dakatar da hakan da wasu sabbin dokoki. Ita kuwa kasar Kenya ta dakatar da hukuncin na kisa ne kwata-kwata a nata bangaren. Baya ga Najeriyar dai akwai ma kasashe irinsu Sudan ta Kudu da Somaliya da har yanzu ke aiwatar da hukuncin.