Amnesty ta binci yakin Mosul
July 11, 2017Rahoton na Amnnesty na cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa tsakiyar Mayu, an kai hare hare 45 wanda yayi sanadiyar mutuwar fararen hula 426. A watan Oktoban shekara ta 2016 ne dakarun gwamnatin Iraki dake samun goyoyn bayan sojojin Amirka, suka kaddamar da yaki na musamman a kan mayakan IS da nufin maida birnin Mosul a hannun gwamnati.
Binciken kungiyar ya gano yadda aka gallazawa fararen hula da dama, wanda yayi sanadiyar darurwan mutane kaurace wa birnin Mosul. kungiyar ya bukaci hukunta wadan da aka samu da hannu a aikata laifukan da suka zarta misali a kan wadanda basuji ba ba su gani ba.
Wannan dai na zuwane bayan da dakarun gwamnatin Iraki suka kaddamar da hari kan wasu gungun mayakan IS dake samun mafaka a kudancin birnin Mosul, somamen dai na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnati ta ayyana nasarar kakkabe kungiyar IS a birnin.