Amnesty International ta zargi kasashen yamma da watsi da yan gudun hijira na Iraki | Labarai | DW | 24.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty International ta zargi kasashen yamma da watsi da yan gudun hijira na Iraki

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta zargi kasashen yammacin duniya da yin watsi da batun yan gudun hijira na Iraki.Kungiyar tace yakin kasar Iraki ya haddasa samarda yan gudun hijira mafi muni a YGTT tun tarwatsa alummar Palasfinwa a 1948.

Amnesty tace kasashen Syria da Jordan suna iyaka kokarinsu na tsugunad da yan Irakin yayinda kasashen yamma da dama cikinsu harda wadanda suka mamaye Irakin suke ci gaba da yin kunnen uwar shegu game da halinda jamaar kasar Irakin suka fada ciki.Cikin wani rahoto kuma na Hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD yan Iraki fiye da miliyan 2 aka tilastawa neman mafaka a kasashe makwabta.Miliyan 1 da dubu dari 2 a Syria yayinda 100,000 suke Jordan.