Amirkawa na ƙara mutuwa a Afganistan | Labarai | DW | 29.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirkawa na ƙara mutuwa a Afganistan

A dai-dai lokacin da faɗa ke ƙara zafafa tsakanin 'yan Taliban da sojojin ƙawance, ministan tsaron Jamus ya kai ziyara a ƙasar.

default

Karl-Theodor zu Guttenberg a Kabul

Ministan tsaron Jamus Karl-Theodor zu Guttenberg da shugaban majalisar dokokin ƙasar Norbert Lammert sun kai ziyarar ba zata a ƙasar Afganistan. Shugabannin biyu suna ziyartan dakarun Jamus dake yankin Mazar-sharif a ƙasar ta Afganistan. A yayinda yau za su isa birnin Kabul, shugaban majalisar dokokin Jamus Norbert Lammert ya bayyana cewa dakarun Jamus na da cikekken goyon bayan majalisar ƙasar a aikin da suke yi a Afganistan. Da yake jawabi kwamandan dakarun Jamus dake ƙasar ta Afganistan, yace fitar da takardun sirri na aiki da dakarun mamaya ke yi a Afganistan, wanda shafin sadarwa na Wikileak ya yi, wata babbar barazanace ga aikinsu.

A wani labarin da yahsafi yaƙin Afganistan, an hallaka dakarun Amirka shida. Wata sanarwar da kakakin sojan ƙungiyar tsaro ta NATO a Afganistan ya bayar, yace dakaru uku sun hallaka a wata karawa da Taliban, yayin da saura uku kuwa sun gamu da ajalinsu lokacin da wani bam ya tashi da su. Ko da jiya madai Taliban ta kai hari a sansanonin sojin Amirka biyu, inda ta jikkata sojojin, kana aka kashe yan Taliban 24 da kama wasu biyar kamar yadda sojin NATO suka sanar. A dai dai lokacin da yaƙin ke ƙara ɗaukan lokaci ana samun ƙaruwar mutuwar dakarun mamaya. Izuwa yanzu wata ƙungiya dake lissafi adadin sojin dake mutuwa a Afganistan da Iraƙi, tace a bana kaɗai an hallaka dakarun ƙasashen yamma 471 abinda yanuna ƙaruwansu, domin a bara waɗanda aka raunata da kaɗan suka zarce hakan. Wannan dai itace shekarar da sojin ƙawance suka fi mutuwa a Afganistan, tun shekaru tara da suka hamɓare gwamnatin Taliban.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal