1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka:Tom Price ya yi marabus

Abdourahamane Hassane
September 30, 2017

Sakataran kula da harkokin kiwon lafiya na Amirka Tom Price ya yi marabus, sakamakon abin da gwamnatin Donald Trump ta kira tabargaza na yi amfani da jiragen sama, masu tsada wajen yin tafiye-tafiye na ayyukan gamnati.

https://p.dw.com/p/2l0Up
USA - Gesundheitsminister Tom Price
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Tom Price dai shi ne mutum na bakwai cikin manyan jami'an gwamnatin Amirka wadanda aka tilastawa barin mukaminsu tun zuwan gwamnatin Donald Trump. Masu aiko da rahotannin sun ce ministan ya fuskancin fushin shugaba Donald Trump ne game da rashin nasara da gwamnatin ta gaza cimma na kawo sauye-sauye a kan tsarin kiwon lafiyar wanda tsofuwar gwamnatin Barack Obama ta amince da shi.