Amirka zata tura wakiliyarta ta musamman zuwa Khartoum | Labarai | DW | 25.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka zata tura wakiliyarta ta musamman zuwa Khartoum

Shugaban Amirka GWB zai tura wata wakiliyar sa ta musamman zuwa Sudan don matsa lamba ga shirin girke dakarun MDD a lardin Darfur mai fama da rikici. A halin da ake ciki wakiliyar ma´aikatar harkokin wajen Amirka akan nahiyar Afirka Jendayi Frazer ta sanar cewa a yau juma´a zata tashi zuwa birnin Khartoum. A cikin sanawar da ta bayar Frazer ta ce dole ne a dauki sahihan matakan kare al´umar yankin na Darfur daga kisan kare dangi da ake yi a can. Tuni dai Amirka da Birtaniya suka gabatarwa kwamitin sulhun MDD wani daftarin kuduri game da tura sojoji dubu 17, don maye gurbin dakarun kungiyar tarayyar Afirka da aka girke a Darfur dake yammacin Sudan. Har yanzu kuwa gwamnatin Sudan na adawa da girke dakarun na MDD. A ranar litini mai zuwa kwamitin sulhu zai zama na musamman kan wannan batu.