Amirka zata kara yawan dakarun ta a yakin da ta ke yi da ´yan tarzoma | Labarai | DW | 20.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka zata kara yawan dakarun ta a yakin da ta ke yi da ´yan tarzoma

Shugaban Amirka GWB ya fadawa wani taron manema labarai a birnin Washington cewa yana duba yiwuwar kara yawan dakarun kasar sa a Iraqi da Afghanistan. Ya ce dalilin yin haka shi ne yakin da ake yi da ta´addanci wanda ya ce wani kalubale ne da za´a dade ana fuskanta.

A yau dai sabon sakataren Amirka Robert Gates ya kaiwa dakarun kasar ziyara a birnin Bagadaza. Shugaba Bush ya dora masa nauyin sake fasalta dubarun sojin kasar a Iraqi. A kuma halin da ake ciki rundunar sojin Amirka ta mikawa dakarun tsaron Iraqi ragamar tafiyar aikin tabbatar da tsaro a lardin Najaf mai tsarki ga mabiya darikar Shi´a.