1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka zata fara janye dakarunta daga Iraƙi a ƙarshen wannan shekara

September 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuBT

Shugaban Amirka GWB ya sake yin watsi da kiran da ake yi dangane da janye dakarun Amirka gaba daya daga Iraqi to amma ya ce sojoji dubu 30 zasu koma gida kafin watan yuli na shekara mai zuwa. Dubu 5 da 700 daga cikin zasu bar Iraqi kafin bukin kirsmeti na wannan shekara. A cikin wani jawabi da yayiwa al´umar Amirka Bush ya ce ya amince da rage yawan sojojin kamar yadda babban kwamandan Amirka a Iraqi Janar David Patraeus ya bawa majalisar dokoki shawara.

Bush ya ce:

“Bayan na tuntubi hafsohin sojin mu da sauran wakilai na tsaron kasa da kuma jami´an Iraqi da shugabannin jam´iyu a majalisun dokokin na amince da shawarar janar Petraeus. Kuma na umarce shi da amsada Ryan Crocker da su sabunta dubarunsu dangane da Iraqi don mu sake fasalta dabarun mu na soji da na farar hula don su dace da halin da ake ciki.”