Amirka zata ci-gaba da sayarwa Taiwan makamai masu linzami | Labarai | DW | 03.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka zata ci-gaba da sayarwa Taiwan makamai masu linzami

Amirka ta yi watsi da adawar da China ke nunawa game da shirin sayarwa Taiwan daruruwan makamai masu linzami na Amirka. Ma´aikatar tsaron Amirka ta nunarwa majalisun dokokin kasar cewa tana shirin sayarwa Taiwan makamai masu linzami da kudinsu ya kama dala miliyan 421, don taimakawa Taiwan din ta kare kanta daga China. Wani kakakin ma´aikatar harkokin wajen Amirka ya ce shirin zai taimaka Taiwan ta cimma bukatunta na tsaro kuma shirin ya dace da dokokin gwamnatin Amirka da suka shafi huldodi tsakanin ta da Taiwan. A nata bangaren China ta bukaci Amirka da ta soke shirin na sayar da makaman tana mai gargadin cewa shirin na barazana ga zaman lafiya da kwaciyar hankalin yankin.