Amirka zata canza dubarunta don tinkarar rikicin Iraki | Labarai | DW | 21.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka zata canza dubarunta don tinkarar rikicin Iraki

Shugaban Amirka GWB ya gana da wasu janar-janar na kasar akan halin da ake ciki a Iraqi. KO da yake ba´a yi bayani dalla dalla kan batuttuwan da suka tattauna akai ba amma majiyoyin wakilan gwamnati gabanin taron sun ce Bush na shirin yiwa dubarunsa akan Iraqin canje canje, musamman dangane da tashe tashen hankulan da suka ki ci suka ki cinyewa a kasar. Ya ce manufar gwamnatinsa kamar kullum ita ce samun galaba kan masu tada kayar baya tare da gina wata kwakkwarar gwamnati a Iraqin. Bush ya amsa cewar karin yawan dakarun da aka yi a birnin Bagadaza bai daidaita al´amura a birninkamar yadda aka yi fata ba. A cikin jawabinsa ta gidan radiyo da yake yiwa Amirka a kowane mako shugaba Bush cewa ya yi.

“Manufar mu a Iraqi a baiyane take kuma ba ta canza ba. Manufar mu ita ce nasara. Abin da muke yiwa kwaskwarima shi ne salo da dubarun da muka amfani da su don cimma wannan manufa. A kullum kwamndojinmu a kasar suna sauya dubarunsu don tinkarar abokan gaba musamman a birnin Bagadaza.”