Amirka za ta rage sojojinta a Koriya ta Kudu
May 4, 2018Talla
Sai dai sun bayyana cewa batun rage yawan dakarun Amirka baya cikin jadawalin ganawar shugaba Trump da shugaban Koriya ta Arewa a tsakanin karshen watan Mayu ko Yuni. Sai dai ana ganin tattaunawar neman dinke baraka tsakanin Amirka da koriyoyin biyu, zai yi tasirin janye sojojin Amirka dubu 23 da ke jibge a yankin.
Sai dai ana nuna shakku kan cire sojojin Amirka baki daya daga yankin ba tare da samun tabbacin warware matsalar tsaro a tsakanin kasashen biyu ba. Fadar White House da kuma ma'aikatar tsaron Amirka ba su yi martani kan batun shirin rage yawan sojojin Amirka da ke aiki a yankin Koriya ba.