Amirka za ta kara sojojinta a Nijar
October 24, 2017Talla
Wannan mataki na Amirka na zuwa ne kwanani kalilan bayan wasu jerin hare-haren kwantan bauna da wasu 'yan bindiga suka kai kan iyakar Nijar da Mali, inda suka kashe dakarun Amirka hudu tare da wasu sojojin Nijar a farkon watan Oktoba.
A yanzu dai Pentagon na shirin girke karin wasu dakaru 800 a Nijar da wasu sauran kasashen Afirka, da nufin murkushe ayyukan ta'addancin kungiyar IS da ke zama karfen kafa a wasu kasashe da ke gabashi da yammacin nahiyar ta Afirka baki daya.