1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta shawarci kungiyar kasashen nahiyar a kan Venezuela

Zulaiha Abubakar MNA
June 4, 2018

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya sake yin kira ga kungiyar kasashen nahiyar Amirka da su gaggauta dakatar da Venezuela, sakamakon zargin yi wa kundin tsarin mulkin demokradiyya karan tsaye.

https://p.dw.com/p/2yvcK
Venezuela - Venezuela startet eigene Kryptowährung Petro - Präsident Maduo
Hoto: Reuters/M. Bello

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya kuma yi Allah wadai da zaben da aka gudanar a watan da ya gabata a kasar ta Venezuela, wanda ya sake bai wa shugaban kasar Nicolas Maduro damar cigaba da shugabancin kasar.

Da yake mayar da martani ministan harkokin kasashen wajen Venezuela ya zargi kasar Amirka da karya sharuddan zaman taren da kungiyar ta yi tanadi sakamakon takunkumin da ta kakaba wa Venezuelan tun a baya.