Amirka ta yi kira ga Masar da ta saki dan adawa Aiman Nur | Labarai | DW | 24.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yi kira ga Masar da ta saki dan adawa Aiman Nur

Kasar Amirka ta yi kira ga Masar da ta saki dan adawar kuma tsohon dfan takarar shugaban kasar Aiman Nour, wanda a yau asabar wata kotu a birnin Alkahira ta yankewa hukuncin daurin shekaru 5 a kurkuku. Kakakin fadar White House Scott McClellan ya ce wannan hukuncin ya sanya shakku game da sahihancin ikirarin kasar na aiwatar da canje canjen demukiradiya. Kakakin ya ce fadar gwamnatin Amirka ta damu game da hukuncin daurin shekaru 5 da aka yankewa Malam Nour mai sassaucin ra´ayi. Kotun da ta yanke masa wannan hukuncin ta ce ta same shi da laifin amfani da takardun bogi wajen kafa jam´iyarsa ta Ghad. Hukuncin ya sha suka a ciki da wajen kotun, musamman akan titunan babban birnin na Masar. Nour mai shekaru 41 da haihuwa, ya kasance babban mai kalubalantar shugaba Hosni Mubarak a zaben shugaban kasar, wanda shugaba Mubarak din ya lashe.