Amirka ta yi gargadin janye taimakon da ta ke ba Falasdinawa | Labarai | DW | 28.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yi gargadin janye taimakon da ta ke ba Falasdinawa

Shugaban Amirka GWB ya ce za´a rage taimakon da Amirka ke bawa Falasdinawa idan kungiyar masu kishin Islama ta Hamas ta ki rushe bangarenta na masu daukar makami kana kuma ta ki daina yiwa Isra´ila barazana. A lokacin da yake magana a wata hira da tashar telebijin ta CBS, shugaba Bush ya ce gwamnatin Washington ba zata ba da taimako ga wata gwamnati da ke son kawad da babbar abokiyar Amirka ba. Da farko jami´an Amirka sun yi gargadin cewa gwamnatin Washington zata sake yin nazari akan taimakon da take ba Falasdinawa idan aka shigar da Hamas cikin sabuwar gwamnati kamar yadda ake sa rai. A bana Amirka ta ware kudi dala miliyan 240 ga Falasdinawa. A gobe lahadi ne kuma idan Allah Ya kaimu SGJ Angela Merkel zata fara ziyarar aiki a Isra´ila da yankin Falasdinawa to amma ba zata gana da wakilan Hamas ba.