Amirka ta yi fatan ganin an samu shiri da Rasha | Labarai | DW | 13.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta yi fatan ganin an samu shiri da Rasha

Shugaban Amirka Donald Trump ya ce yana fatan Amirka da ma kungiyar tsaro ta NATO su samu sasantawa da Rasha.

U.S. Präsident Trump und NATO-Generalsekretär bei der Pressekonferenz am Weißen Haus (Reuters/J. Ernst)

Shugaban Amirka Donaid Trump da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg.

Yayin wani taron manema labarai da Shugaban Amirka Donald Trump ya yi da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce yana fatan ganin Amirka da ma kungiyar ta NATO sun samu jittuwa da Rasha, inda ya nuna gamsuwarsa kan ganawar da shugabannin diflomasiyyar kasashen biyu suka yi a birnin Mosko yayin ziyarar farko da Rex Tillerson ya kai a kasar ta Rasha.

"Ina tsammanin an samu tattaunawa mai ma'a. Za mu ga sakamako nan gaba, kilan cikin lokaci mai tsawo. Amma kuma sakamakon shi ne mafi muhimmanci ba wai maganganun da aka yi ba. Kuma bisa abubuwan da naji an tattauna, ina iya cewa lamura sun gudana da kyau fiye ma da yadda muka yi zato a wannan ziyara."

Shugaban na Amirka ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ke ziyarar aiki a Rasha.