1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yi barazanar soke kudin taimakon da take bai wa Falasdinawa, idan Hamas ba ta yi watsi da akidarta ta yakan Isra’ila ba.

January 30, 2006
https://p.dw.com/p/BvA9

Fadar White House, ta shugaban gwamnatin Amirka, ta karfafa gargadin da mahukuntan kasar ke yi wa Falasdinawa na cewa, za ta soke duk wasu kudaden taimakon da take ba su, idan kungiyar nan ta abin da ta kira `yan tsatsaurar ra’ayi ta Hamas, ba ta kauce daga manufar da ta sanya a gaba ta ta yakan Isra’ila ba, bayan lashe zaben da ta yi. Kakakin fadar ta White House Scott McClellan, ya fada wa maneman labarai yau a birnin Washington cewa, gwamnatin Amirka ba ta ba da tallafin kudade ga wata kungiyar `yan ta’adda, kuma ba za ta yi haka din yanzu ba. Bugu da kari kuma, ya ce ba za ta ba da tallafin kudi ga kungiyar da ke kira ga ragragaza kasar Isra’ila da kuma yada ayyukan ta’addanci ba.

Amirka dai, inji McClellan, na sane da cewa al’umman Falasdinu na bukatar taimakon agaji, kuma wannan wani hali ne da za ta yi nazarinsa. Za ta dinga dai yin bitar shirye-shiryenta na ba da taimakon ne bisa yadda ababa za su wakana nan gaba.

Tuni dai shugaba Bush da kansa ma, ya yi wannan gargadin, inda ya bayyana cewa, Washington za ta tsai da duk wani taimako ga Falasdinawa, idan kungiyar Hamas ta shiga Hukumar Falasdinawan ba tare da yin watsi da akidarta ta ragargaza Isra’ila ba.

A shekarar bara dai, Amirka ta bai wa Hukumar Falasdinawan taimakon kudi kai tsaye na kimanin dola miliyan 50. Amma ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce ba ta yi wani tanadin taimakon ba kuma, a kasafin kudinta na wannan shekarar. Sai dai akwai wani shirin bai wa Falasdinawan taimakon kudi na kimanin dola miliyan dari da 50 a wannan shekarar, ta kan asusun ba da taimakon raya kasashe ta Amirkan, da wasu dola miliyan 84 kuma, wadda za a bayar ta kan asusun Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ba da taimako da gudanad da ayyukan agaji ga `yan gudun hijiran Falasdinawa a yankin Gabas Ta Tsakiya.