1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yaba da samun sauyi a Zimbabuwe

Gazali Abdou Tasawa MNA
November 22, 2017

Amirka ta bayyana gamsuwarta da yadda al'ummar kasar Zimbabuwe ta kawo karshen mulkin Shugaba Mugabe ta hanyar demokradiyya ba kuma tare da zubar da jinin 'yan kasa ba.

https://p.dw.com/p/2o1mE
Simbabwe Jubel und Feier nach Mugabe Rücktritt
Hoto: picture-alliance/AP/B. Curtis

 A cikin wata sanarwa da ya fitar sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya yi kira ga dukkanin bangarorin siyasar kasar Zimbabuwe da su kasance masu hakuri da juna su kuma kiyaye kundin tsarin mulkin kasar tasu. 

Tillerson wanda ya bayyana saukar Shugaba Mugabe a matsayin wani babban abin tarihi, ya ce a yanzu dama ta samu ga al'ummar kasar ta daukar matakan kawo karshen zaman saniyar ware da kasar ke cikinsa a tsawon wasu shekaru na mulkin tsohon shugaban mai shekaru 93. 

A wannan Laraba ce dai ake sa ran za a rantsar da tsohon mataimakin shugaba Mugaben wato Emmerson Mnangagwa  mai shekaru 75 a matsayin shugaban riko na kasar ta Zimbabuwe.