1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yaba ayyukan Faransa a Sahel

Salissou Boukari
April 24, 2017

Sakataran tsaron Amirka James Mattis da ya kai wata ziyarar aiki a kasar Jibuti, ya yi fatan ganin cewa kasar Faransa za ta ci gaba da yakin da take da 'yan ta'adda a yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/2bm1u
Irak US-Verteidigungsminister Jim Mattis | Ankunft in Bagdad
Sakataran tsaron Amirka Jim Mattis na ziyartar sojojin Amirka a kasashe daban-dabanHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Meghani

Mattis ya jinjinawa kasar Faransa inda ya ce tana kasancewa a inda ya kamata ta kasance da zaran abu ya shafi yaki da ta'addanci. Sakataran tsaron na Amirka ya yi wadan nan kalamai ne yayin wani taron manema labarai a kasar ta Jibuti.

Amirka dai na goyon bayan shirin kasar Faransa na Operation Barkhane a cikin kasashe biyar na yankin Sahel da suka hada da Mauritaniya, Mali, Chadi, Nijar da kuma Burkina Faso, inda ta barwa kasar ta Faransa da ta yi wannan aiki na yaki da 'yan ta'adda a yankin na Sahel.

Amirka ta tallafa wa jiragen yakin kasar ta Faransa da mai, da kuma karfafa musayar bayannai tsakanin sojojin kasashen biyu. A kasar ta Jibuti dai Sakataran tsaron na Amirka ya gana da shugaban kasa Ismaël Omar Guelleh, da kuma babban komandan sojojin na Amirka a Afirka Janar Thomas Waldhauser.