1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta tura sojojin ruwa don hana ´yan Islama tserewa daga Somalia

January 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuVZ
Jiragen ruwan yakin Amirka sun shiga cikin farautar sojojin sa kai na ´yan Islama da ake zargi suna da alaka da kungiyar al-Qaida, wadanda yanzu haka suke kokarin tserewa daga Somalia. Ma´aikatar harkokin wajen Amirka ta ce ta damu game da cewar ´yan takifen ka iya tserewa daga Somalia. Ma´aikatar ta ce ´yan takifen na da alaka da kungiyoyin ta´addanci wadanda ake nema dangane da hare-haren bam da aka kai kan ofisoshin jakadancin Amirka a gabashin Afirka a shekara ta 1998. A dai halin da ake ciki Kenya ta rufe kan iyakarta da Somalia don hana shigar mayakan da makamai cikin kasar ta. A kuma halin da ake ciki KTT ta yi kira ga gwamnatin wucin gadin Somalia da mayakan Islama su shiga tattaunawa don cimma wani shirin wanzar da zaman lafiya.