Amirka ta tsaurara takunkumin da ta sanyawa Sudan
October 14, 2006Talla
Amirka ta fadada takunkumin da take dorawa Sudan. SHUgaba GWB ya ba da dalilin tsaurara matakan da ci-gaba da tashe tashen hankula da keta hakin bil adama musamman a yankin Darfur mai fama da rikici ma yammacin Sudan. Tun a shekara ta 1997 Amirka ta haramta sayen kaya da wasu ayyuka na yiwa jama´a hidima daga kasar ta Sudan. Karin takunkumman da shugaba Bush ya sanyawa hannu ya hada da dukkan harkokin samar da mai da dangoginsa. A lokaci daya kuma Bush ya sanya hannu kan wata takarda wadda ta kebe yankin Darfur daga wannan takunkumi.