1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta shawarci Majalisar Ɗinkin Duniya da ta tura dakaru zuwa Sudan.

May 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buyv

Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya amince tura dakarun kare zaman lafiya zuwa yankin Darfur na ƙasar Sudan cikin gaggawa. Rice, ta kuma bukaci kwamitin da ya zartad da wani ƙudurin da Amirkan ta tgabatar, wanda zai bai wa dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniyar damar karɓar jagorancin ayyukan kare zaman lafiya a yankin na Darfur daga rundunar Ƙungiyar Tarayyar Afirka.

A nasa ɓangaren, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya ce kamata ya yi a angaza wa sauran kungiyoyin ’yan tawayen da suka ƙaurace wa yarjejeniyar ta Darfur da su sanya hannu a kanta. A ran juma’ar da ta wuce ne dai, gwamnatin Sudan da babban reshen ƙungiyar ’yan tawayen SLM suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu a birnin Abujan Najeriya.