Amirka ta saki wasu ´yan Saudiyya 14 daga sansanin Guantanamo | Labarai | DW | 24.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta saki wasu ´yan Saudiyya 14 daga sansanin Guantanamo

An saki wasu ´yan Saudiyya 14 daga sansanin sojin Amirka na Guantanamo dake kasar Cuba, kuma yanzu haka an mika su ga hukumomin kasar su. Wata sanarwa da ma´aikatar tsaron Amirka ta bayar ta ce an saki daya daga cikin mutanen ne saboda jami´an Amirka sun tabbatar cewa yayi watsi da akidar nuna gaba daAmirka. Sannan sauran kuma an sake su ne bayan wani nazari da aka yi akan su ya gano cewar ana iya mika su ga hukumomin kasar su. Sakin su ya kawo yanzu yawan firsinonin da Amirka ta sako daga sansanin na Guantanamo ya zuwa mutum 310. Yanzu haka dai saura firsinoni 450 da har yanzu ake tsare da su a wannan sansanin bisa zargin ta´adanci ko kuma kasancewa barazana ga Amirka.