Amirka ta sake gargadin Iran a game da shirin ta na Atom | Siyasa | DW | 19.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amirka ta sake gargadin Iran a game da shirin ta na Atom

Kasar Amirka ta yi wa Iran gargadi a game da hukuncin da za ta fuskanta, idan ta ci gaba da shirin ta na kera makaman atom

default

Shugaban Amirka, Baarack Obama

Sakataren Tsaron Amurka Robert Gates yace Ashirye Amurka ta ke ta tauki jeerin matakai game da shirin Iran .yace ko dai ayi tunanen cewa Iran zata gagari Amurka .Husseina Jibrin Yakubu na dauke da ƙarin bayani.

Sakataren tsaron Amurka,Robert Gates yace a watan janairu ya rubuta wasu jerin matakai da ya kamata a dauka bayan da gwamnatin Obama ta bayad da shawarar ƙara yin matsin lamba game da shirin Nukiliyar Iran.

Babban hafsan sojin ƙasar, Admiral Mike Mullen shi kuma ya ƙara muryarsa ga bukatar ɗaukar matakin soji in har Iran ta ci gaba da yin kunnen uwar shegu ga kiraye-kirayen da ake mata da ta dakatar da shirinta na Nukiliya.

Shima shugaban Amerika, Barack Obama yace muddin Iran din ta ki jin gargadin da ake mata to kuwa zata dandana kudar ta.

Sai dai kuma a bangaren ministan harkokin wajen Iran Manouchehr Mottaki, cewa yayi a shirye ƙasarsa take ta shiga tattaunawa tare da dukkannin mambobi 15 na kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya , idan zasu maida hankali ga bukatar yin musayan makamashi.

A watan oktoban bara sai da a ka zayyana wata jarjejeniya da ta tanadi ba wa Iran makamashi domin aikin ta na Nukiliya ta yin jigilar Ureniyom daga Iran da kuma bata makamashin da aka tace a Rasha da Faransa.

Amma an samu saɓani game da nacewar da Iran ke yi da cewa sai dai a yi wannan musayar a cikin gidanta, sharaɗin da gaggan ƙasashen duniya suke yin fatali dashi. Amurka,Burtaniya,da Faransa sun bayyana aniyarsu na ƙaƙaɓa ƙarin takunkumi a kan Iran.

Sai kuma Rasha da China da ke da ikon hawa kujerar naƙi. suna jan ƙafa wajen ba da goyon bayansu ga wannan mataki.

Shugaban Amerika Obama yace irin take-taken China a game da batun takunkumin kan Iran ko kadan ba daidai bane.

Adai halin yanzu ana cigaba da ta da jijiyiyin wuya sakamakon matakin Amurka na sanar da manufofinta game da shirin Nukiliyar Iran.

Ministan harkokin wajen Iran, Mottaki yace zasu mai da martani ga duk wani matakin kai harin akan Iran.

Ya ƙara da cewa duk wanda zai shirya wannan zai ɗanɗana ƙuɗarsa.

Husseina Jibrin Yakubu

Edita: Umaru Aliyu