Amirka ta nemi ′ya′yanta da su kaurace wa Kabul | Labarai | DW | 11.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta nemi 'ya'yanta da su kaurace wa Kabul

Ofishin jakadancin Amirka a kasar Afganistan yayi gargadin cewar mai yiwuwa ne mayakan sa kai su kai wani hari a kan Amerikawa da ke wani otel a Kabul.

Ofishin jakadancin ya kara da cewar ya na shawarartar duk wasu Amerikawa da su kaucewar otel din tare da zama cikin shirin ko ta kwana a yayin da suke halartar gidajen otel a birnin na Kabul.

Shi dai wannan gargadin na zuwa ne bayan wasu rokoki da aka harba a yankin da ofisoshin Diplomasiya suke a ranar asabar din nan jim kadan bayan Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya gudanar da wani taro da Shugabanin kasar ta Afghanistan a birnin Kabul.