Amirka ta kare shirin ta na sa ido a harkokin aikewa da kudi a duniya | Labarai | DW | 24.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta kare shirin ta na sa ido a harkokin aikewa da kudi a duniya

Sakataren kudin Amirka John Snow ya kare wani shirin sirri na sa ido kan harkokin aikewa da kudade a duniya. Mista Snow ya kira shirin da cewa wani gagarumin aiki ne na yaki da ta´addanci. Kusan shekaru biyar bayan hare haren 11 ga watan satumban shekara ta 2001, gwamnatin Amirka ta yi ta sa ido a boye ga harkokin aikewa da kudi a duniya da aka fi sani da SWIFT. Duk da kokarin da aka yi na rufe wannan shiri, a jiya juma´a jaridar New York Times ta bayanawa duniya wannan shiri. Ma´aikatar kudin Amirka ta ce shirin ya ta´allaka akan bayanai na wadanda ake zargi da aikin ta´addanci. Amma wakilan jam´iyar democrat sun yi tir da shirin suna masu cewa wata barazana ce ga Amirkawa.