Amirka ta kai hari a wani yanki dake arewacin Somalia | Labarai | DW | 02.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta kai hari a wani yanki dake arewacin Somalia

Jami´ai a arewacin Somalia sun ce jiragen ruwan yakin Amirka sun kai hari akan wani kauye dake cikin tsaunuka, inda ake kyautata zato wani mai tsattsauran ra´ayin Islama ya kafa sansani. Rahotanni sun ce dan ta´addan da ake magana kan shi wani dan kungiyar al´Qaida ne da ake zargi da hannu a hare haren bama-bamai da aka kaiwa ofisoshin jakadancin Amirka a Kenya da Tanzania a shekarar 1998. babu wani rahoto game da rayukan da suka salwanta sakamakon harin da jiragen ruwan yakin Amirka suka kai a jiya da daddare.