1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an kasar kwango sun rasa izinin shiga Amirka

Salissou Boukari
June 22, 2018

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta sanar da hana wasu manyan jami'an gwamnatin Kwango DRC shiga kasarta, bisa zarginsu da hannu cikin badakalar cin hanci a da ke kawo cikas ga zaben kasar.

https://p.dw.com/p/303fj
USA Ankündigung Austritt aus UN-Menschenrechtsrat | Nikki Haley & Mike Pompeo
Hoto: Reuters/T.S. Jordan

Sai dai sanarwar ta ma'aikatar harkokin wajen na Amirka ba ta fadi adadin wadannan jami'an gwamnatin ta Kwango ko kuma sunayensu ba, inda ta ce ko ma ba a sanar da sunayan mutanen ba, amma kuma hakan wani babban sako ne, domin cin hanci abu ne da ba za a yarda da shi ba, wanda ke dabaibaye manyan ma'aikatu na kasar.

Amirka dai ta sha alwashin yaki da cin hanci tare kuma da goyon bayan tsarin gudanar da zabukan kasar ta Kwango ta yadda ake fatan ganin a karon farko wani shugaba da ya gama mulki zai damka wa sabon shugaban da aka zaba ragamar mulki a kasar ta Kwango.