Amirka ta gayyaci jami´an Majalisar Dinkin Duniya zuwa sansanin Guantanamo | Labarai | DW | 29.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta gayyaci jami´an Majalisar Dinkin Duniya zuwa sansanin Guantanamo

Amirka ta gayyaci wasu wakilan MDD zuwa sansaninta na Guantanamo inda ta ke tsare da mutanen da ta ke zargi da aikata ta´addanci. Wata sanarwa da ma´aikatar harkokin waje a birnin Washington ta bayar ta nunar da cewa za´a bawa masanan na MDD damar ganewa idonsu halin da mutanen da ake tsare da su a wannan sansani ke ciki, musamman bayan zargin da ake yi cewa ana keta hakkin su. Tun kimanin shekaru 4 da suka wuce jami´an MDD ke neman Amirka ta ba su izinin kai ziyarar ganewa ido a sansanin na Guatanamo dake kasar Cuba.