1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta gaiyaci ƙasashen Larabawa da dama zuwa taron yankin GTT

Kasar Amirka ta ce zata gayyaci kasashen Larabawa da dama ciki har da Syria zuwa gun taron zaman lafiyar yankin GTT da za´a gudanar a karshen wannan shekara. Sakatariyar harkokin wajen Amirka C.-Rice ta ba da wannan sanarwa bayan wani taro a birnin New York na bangarorin hudu dake daukar nauyin shirin samar da zaman lafiya a GTT wato Amirka, MDD, KTT da kuma Rasha. A cikin sanarwar bayan taron bangarorin hudu sun nuna goyon bayan su ga taron wanda ta kira da ake sa ran gudanarwa cikin watan nuwamba a birnin Washington. Rice ta ce da jan aiki gaba, inda ta kara da cewa.

Rice:

“Kokarin da Falasdinawa da isra´ila ke yi na kawo karshen rikicin na kara samun goyon baya. Akwai jan aiki gaban mu yanzu. Kuma kamar yadda ya ke a kullum a dangane da GTT, ya kamata a san cewa aikin da ke gaban mu mai wuya ne matuka.”

Daga cikin kasashen Larabawa da ake sa ran gayyatar su zuwa taron, Masar da Jordan ne kadai suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Isra´ila.