1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta dage takunkumi ga Chadi

Abdoulrazak Garba Babani RGB
April 11, 2018

Gwamnatin Amirka ta bayar da sanarwar dage dokar da ta sanya ga kasar Chadi na hana al'ummarta shiga Amirkan, bayan da ta yi na'am da ingantar harkokin tsaro da ta ce ya zo dai-dai da sharuddan da ta gindaya.

https://p.dw.com/p/2vtIv
Sudan Khartum Idriss Deby Präsident Tschad
Hoto: picture-alliance/dpa/E. Hamid/Ausschnitt

 

Shugaban kasar Amrika Donald Trump ya sanar da cewa kasar Chadi a yanzu ta inganta fannin tsaro, saboda haka a yanzu kofa a bude ta ke don bai wa al'ummar Chadi takardar izinin shiga ta visa. Ministan harkokin wajen kasar Chadi Charif Mahamat Zéne ya yaba da jin wannan labari, inda ya ce kasar ta gamsu da matakin cire sunanta daga cikin jerin kasashen da aka dakatar da su daga shiga Amirkan. Mahamat Kachalla wani jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Chadi ya ce ya yi matukar jin dadin wannan sanarwa, domin dama haramtawa 'yan kasar zuwa Amirka ya haifar da nakasu ga harkokin shige da fice a tsakanin kasashen biyu, kuma babu wata matsala a tsakani face wani abu kawai na son zuciya. 

Dan majalisar dokokin kasar ta Chadi Saleh Mustafa ya ce al'ummar Chadi sun yi matukar farin ciki da dage wannan doka, kuma a shirye kasar take wajen hada karfi da karfe da Amirka a yaki da ayyukan ta'addanci. Dage wannan takunkumi abu ne mai matukar muhimmanci domin kasar Amirka wata matattarace ta al'umma daban-daban da ke iya samar da ayyukan ci-gaba kamar yadda masana ke wa al'amarin fassara. Kasar Chadi ta kasance cikin kasashe takwas da Amirka ta sanya musu takunkumi na hana shigar al'ummarsu kasarta, sauran kasashen sun hada da Iran da Libiya da Siriya da Somaliya da Yemen da Banizuwela da kuma Koriya ta Arewa.