Amirka ta ce lalle ta sake kai hari a kudancin Somalia | Labarai | DW | 25.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta ce lalle ta sake kai hari a kudancin Somalia

Amirka ta tabbatar da cewa a karo na biyu ta sake kai farmaki ta sama akan ´yan al-Qaida dake kudancin Somalia a jiya laraba. Wadanda suka shaida abin ya faru sun rawaito cewar jiragen saman yakin Amirka sun yi ruwan bama-bamai akan wasu wurare a cikin garuruwa biyu dake kusa da kan iyakar Somalia da Kenya. Makonni biyu da suka wuce jiragen saman yakin Amirka sun kai hari akan abin da Washington ta kira koran ´yan Al-qaida dake tserewa tare da dakarun ´yan Islama wadanda dakarun gwamnatin Somalia da na Ethiopia suka fatattake su. A lokaci daya kuma jakadan Amirka a Kenya Michael Ranneberger ya gana da shugaban kotunan Islama Sheikh Sharif Ahmed a birnin Nairobi a wani mataki na samun hadin kai da gwamnatin wucin gadi a Mogadishu.